Turai

Kasashen Turai sun amince su karbi 'yan ci-rani

Wasu daga cikin 'yan ci-ranin da ke neman ingantacciyar rayuwa a Turai
Wasu daga cikin 'yan ci-ranin da ke neman ingantacciyar rayuwa a Turai REUTERS/Lucy Nicholson

Kasashen Turai 14 ne suka bayyana amincewa da wani sabon shiri da suka bayyana cewa na jinkai ne, wanda ya tanadi raba ‘yan ci-rani a tsakaninsu, to sai dai kasar Italiya ta yi kakkausar suka a game da shirin wanda ta bayyana shi da cewa zai karfafa wa baki guiwa ne don ci gaba da kwarara a yankin na Turai.

Talla

Wannan dai na kunshe ne a sanarwar bayan taron da kasashen na Turai suka gudanar a birnin Paris karkashin jagorancin shugaban Faransa Emmanuel Macron, inda suka tattauna kan samar da sabon tsarin raba ‘yan ci-ranin da suka yi nasarar tsallaka teku tare da shiga yankin na Turai, wadanda a karkashin doka ba ta yadda za a iya komawa da su a kasashen da suka fito.

Kasashen Turai 14 ne suka amince da shirin raba ‘yan ci-ranin a tsakaninsu, yayin da wasu 8 suka ce ba za su karbi ‘yan ci-ranin ba, amma za su bayar da gudunmawa ta wata fuska.

Daga cikin wadanda suka amince da shirin akwai Faransa da Jamus da Finland, Luxembourg da Portugal da Lithuania da Crotia da kuma Ireland, shawarwar da nan take Ministan Cikin Gidan Italiya mai tsatsauran ra’ayi Matteo Salvini ya ce, kasar ba za ta amince da ita ba.

An gudanar da wannan taro ne a daidai lokacin da gwamnatin Italiya ta jaddada haramta wa jirgin ruwan nan da kungiyoyin agaji ke amfani da shi domin ceto ‘yan ci-rani a kan teku wato Sea Watch damar gudanar da ayyukansa a tekun Mediterranean.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.