Birtaniya

Ranar 31 ga Oktoba Birtaniya za ta fice daga cikin EU - Johnson

Sabon Fira Ministan kasar Birtaniya Boris Johnson.
Sabon Fira Ministan kasar Birtaniya Boris Johnson. REUTERS/Toby Melville

Sabon Fira ministan Birtaniya, Boris Johnson ya sha alwashin kammala ficewar kasar daga kungiyar Turai ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa.

Talla

Johnson ya sha alwashin ne bayan samun nasarar da yayi a zaben shugabancin Jam’iyyar Conservative.

Boris Johnson ya samu kuri’u 92,153, yayinda abokin takararsa Jeremy Hunt ya samu kuri’u 46,565.

Tuni dai shugabannin kasashen duniya suka aike da sakwannin taya murna ga sabon Fira ministan na Birtaniya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar Boris Johnson zai zama gagarumin shugaban, yayin da shugaba Emmanuel Macron ya bayyana aniyar aiki tare da shi.

Fira ministan Italiya kuwa Matteo Salvini ya yiwa Johnson fatan alkhairi, yayin da kungiyar kasashen Turai tace za tayi aiki tare da sabon Fira ministan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI