Birtaniya

Birtaniya za ta fice daga EU a cikin watan Oktoba- Johnson

Sabon Fira Ministan kasar Birtaniya Boris Johnson
Sabon Fira Ministan kasar Birtaniya Boris Johnson REUTERS/Hannah McKay

Sabon Firaministan Birtaniya, Boris Johnson ya yi alkawarin fitar da kasar daga gungun kasashen Turai a ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa ba tare da wani inda-inda ba. Tuni Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci sabon Firaministan da ya gabatar mata da cikakken bayani kan tsarinsa na ficewar kasar daga EU.

Talla

A yayin gabatar da jawabinsa na farko a fadar Downing Street mai lamba 10, sabon Firaminista, Boris Johnson ya yi alkawarin cimma sabuwar yarjejeniya da mahukuntan Kungiyar Trayyar Turai.

Bayan Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II ta amince da shi a matsayin sabon Firaminsta a wannan Laraba, Johnson ya bayyana muradunsa, inda ya jaddada cewa, dole ne a mutunta kuri’ar ficewar kasar daga Tarayyar Turai.

Johson ya bayyana cewa, yana da duk wani kwarin guiwa kan cewa, nan da kwanaki 99, za su kai ga gaci, yana mai cewa, al’ummar Birtaniya sun gaji da zaman dako.

Johnson wanda shi ne sabon shugaban Jam’iyyar Conservative, ya ce, da kansa zai jagoranci fafutukar samar da sauyin da yake fatan gani a kasar.

Tsohuwar Firaminstar kasar Theresa May wadda ta gaza fitar da Birtaniya daga kasashen Turai, ta yi wa Johnson da gwamnatinsa fatan alheri kan abinda suka sanya a gaba.

Gabanin jawabinta na ban-kwana, Uwargida May ta amsa tambayoyin karshe daga ‘yan majalisun kasar, yayinda ta fice daga majalisar cikin wani yanayi na tausayi tare da yi mata sowa da tafi don jinjina mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI