Turai

EU ta ki amicewa da bukatar sabon Firaministan Birtaniya

Sabon Fira Ministan kasar Birtaniya Boris Johnson
Sabon Fira Ministan kasar Birtaniya Boris Johnson Isabel Infantes / AFP

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta ki amincewa da bukatar sabon Firaministan Birtaniya Boris Johnson da ke neman sake tattaunawa kan yarjejeniyar ficewar da suka cimma da tsohuwar Firaminista Theresa May.

Talla

Shugaban Hukumar Gudanarwar EU Jean-Claude Juncker ya jaddada matsayar kungiyar yayin ganawar da suka yi da sabon Firaministan ta wayar tarho.

Juncker ya ce, yarjejeniyar ta Brexit da suka cimma da tsohuwar Firaminista May, ita ce mafi kyau kuma da ta yi daidai da tsare-tsaren kungiyar kasashen Turan.

Kafin gabatar da bukatar yi wa yarjejeniyar ta Brexit kwaskwarima, sai da Boris Johnson ya yi gargadin cewa, ka’aidojin da ke cikinta za su yi wa tattalin arzikin Birtaniya illa, don haka idan har sake tattaunawa kan ka’idojin bai yiwu ba, basu da zabi illa ficewa daga cikin kungiyar kasashen Turan ba tare da cimma wata yarjejeniya ba a ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa.

Sabon Firaministan na Birtaniya ya kuma yi barazanar dakatar da biyan kudaden rabuwa na Dala biliyan 49 ga EU, domin amfani da su wajen taron yanayin da tattalin arzikin kasar zai shiga bayan ficewa daga kungiyar ba tare da yarjejeniya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.