Bakar fatar Amurka ta farko da ta lashe kyautar Nobel ta mutu

Toni Morrison,Bakar fatar Amurka ta farko da ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel
Toni Morrison,Bakar fatar Amurka ta farko da ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel Getty Images/Daniel Boczarski/FilmMagic

Mace ta farko, bakar fatar Amurka, marubuciya da ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel, Toni Morrison, ta rasu a jiya Talata tana da shekaru 88, bayan gajeruwar jinya.

Talla

Wata sanarwa daga iyalin Morrison ta ce marubuciyar ta rasu a tsanake, kewaye da ‘yan uwa da abokan arziki da masoya, bayan gajeruwar jinya da ta yi.

Morrison ta wallafa litattafai 11, wadanda da daman su ke yin tsokaci ne kan rayuwar bakar fatar Amurka, a sana’ar adabin turancin Ingilishi, mai cike da kyaututtuka da tukuici data shafe shekaru 60 cikinta.

Ta wallafa wakokin zube ta jawabai tare da rubuta mukala da dama a lokuta dabam – dabam, kuma ana girmama ta saboda tsatsauran matsayinta kan abin da ya shafi wariyar launin fata, da kare hakkin dan adam, sannan ba ta fargabar yin tsokaci kan ko wane irin batu na siyasa.

A shekarar 1988, ta lashe kyautar Pulitzer, da ta litattafai na Amurka, wato American Book Award, kan littafinta mai taken ‘Beloved’, wadda ta yi game da yakin basasan Amurka na 1860, labarin wani bawa da ya tsere daga Kentucky zuwa Ohio.

An haifi Toni Morrison a garin Ohio a ranar 18 ga watan Fabrairun 1933, kuma littafin ta na farko shine ‘The Bluest Eyes”, wadda aka wallafa a 1970.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI