Za ku ja wa kan ku idan kuka taimaka wa Venezuela - Bolton

John Bolton,mai baiwa shugaban Amurka shawara kan tsaro
John Bolton,mai baiwa shugaban Amurka shawara kan tsaro JOE RAEDLE / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP

Mai baiwa shugaban Amurka shawara kan tsaro John Bolton, ya ce takunkuman karya tattalin arzikin da suka kakabawa Venezuela, zai shafi duk kasar da ta taimaka mata.

Talla

Bolton ya yi gargadin ne a Lima babban birnin kasar Peru, inda kasashe akalla 60 mafi akasari da ke adawa da gwamnatin Nicolas Maduro, ke halartar taro kan yadda za a kawo karshen rikicin siyasar kasar Venezuela.

Tun a watan Janairu rikicin ya kazanta, bayan da jagoran ‘yan adawa Juan Guaido ya bayyana kansa a matsayin halastaccen shugaban kasar ta Venezuela, wanda kuma kasashe akalla 50 suka goyi bayansa, ciki harda Amurka da wasu manyan kasashen Turai da kuma kasashen Latin na nahiyar kudancin Amurka da Venezuelar ke ciki.

A dai jiya Talata ne Amurka ta ce za ta amfani da dukkanin hanyoyin da suka dace wajen kawo karshen shugabancin Nicola Maduro, bayan da ta bada umarnin kwace dukkanin kadarorin kasar da ke hannunta.

Kawo yanzu Venezuela ta shafe shekaru biyar tana fama da durkushewar tattalin arzikinta, abin da ya haifar da karancin abinci da magunguna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.