Isa ga babban shafi
Amurka

Trump zai haramtawa bakin-haure shaidar zama 'yan kasa

Jerin gwanon dubban bakin-haure daga kasashen yankin Latin, yayin tunkarar Amurka da nufin shiga kasar domin zama da samunguraben ayyukan yi. 27/10/2018.
Jerin gwanon dubban bakin-haure daga kasashen yankin Latin, yayin tunkarar Amurka da nufin shiga kasar domin zama da samunguraben ayyukan yi. 27/10/2018. Reuters/Ueslei Marcelino
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da shirin kafa dokokin da za su haramta baiwa bakin-haure samun takardun izinin zama na din-din-din da kuma na shaidar zama ‘yan kasa.

Talla

Shirin na gwamnatin Amurka babban koma baya ne ga fatan zama ‘yan kasa da miliyoyin bakin-hauren da ke gudanar da wasu kananan ayyuka a kasar ke da shi.

Zalika shirin zai kuma rufewa bakin-hauren kofofin samun damar shiga Amurka domin amfana da kananan guraben ayyuka, da sauran ababen more rayuwa da suka hada da lafiya da kuma ilimi.

Sabuwar dokar da shugaba Trump ke shirin kafawa za ta shafi akalla bakin-haure miliyan 22 masu kananan ayyuka dake da takardun izinin zama a kasar, da kuma wasu Karin ‘yan ci ranin miliyan 10 da rabi da suka dade zaune a Amurka ba tare da izini ba.

Cikin watan Mayun da ya gabata shugaban Amurka Donald Trump yace kasar na bukatar tarin baki-haure, amma wadanda suka kware akan sana’o'i daban daban.

Trump ya bayyana haka ne yayin gabatar da sabon shirin gwamnatinsa dangane da karbar baki.

Shugaban yace sabon shirin zai bada damar kara yawan irin wadannan baki kwararru daga kashi 12 zuwa kashi 57 ko fiye da haka, domin ganin Amurka ta tsaya daidai da sauran kasashen duniya.

Trump ya kara da cewa Amurka na alfahari da bude kofar da za ta yi, amma dole wadanda za su amfana da wannan shirin ya kasance kwararru ne wadanda kuma suka iya Turancin Ingilishi da za su zana jarabawa kafin samun damar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.