Isa ga babban shafi
Faransa

An fara share gubar dalma a mujami'ar Faransa

Mujami'ar  Notre-Dame da ke birnin Paris na Faransa
Mujami'ar Notre-Dame da ke birnin Paris na Faransa Rafael Yaghobzadeh/Pool via REUTERS
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Ahmed Abba
1 min

Masu aikin sake gina mujami’ar Notre Dame ta birnin Paris na kasar Faransa sun soma aikin share gubar dalma a kewayen mujami’ar wadda gobara ta ci a watannin baya.

Talla

Yanzu haka an kafa shingaye a harabar mujami’ar da kewayenta, yayinda masu aikin sharar da manyan motoci ke ta wanke mujami’ar domin kakkabe gubar dalmar baki daya.

Tun bayan konewar mujami’ar a watan Afrilu, masana suka yi ta kashedin cewar,  gubar dalma za ta yi illa ga lafiyar al’ummar da ke makwabtaka da mujami'ar.

Za a yi amfani da na’urorin shara na zamani wajen aikin mujami’ar da aka kiyasta ya kai murabba’in mita 10 da 200, kuma ana sa ran kammala aikin kafin ranar 23 ga watan Agusta da muke ciki.

An dai tara miliyoyin Dala don sake gina mujami’ar ta Notre Dame mai dumbin tarihi, yayinda shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya sha alwashin sake gina ta nan da shekaru biyar masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.