Isa ga babban shafi

Ana iya ba hammata isa tsakanin bakin - haure a jirgin agaji

Wasu bakin - haure a kwale - kwalen ceto
Wasu bakin - haure a kwale - kwalen ceto Anne CHAON / AFP
Zubin rubutu: Michael Kuduson
1 Minti

Ana iya samun barkewar rikici tsakanin bakin – hauren da ke makale cikin jirgin agajin da ya ceto su daga tekun Italiya, kamar yadda shugaban kungiyar agajin da ke tafiyar da jirgin ya yi kashedi a ranar Laraba.

Talla

Shugaban kungiyar agaji ta Proactiva Open Arms, Oscar Camps, ya ce bakin - hauren da ke ciki jirgin ruwan na iya ba hammata – iska a kowane lokaci daga yanzu, kuma hakan zai kasance abin takaici.

A halin da ake ciki, ma’aikata 19 da ke ciki wannan jirgi, wanda ke barin tsibirin Lampedusa, na tekun Italiya da bakin – haure 147 da aka ceto daga kwale – kwale da dama a tekun Mediterranean a wannan wata, na fuskantar kalubalen shawo kan tashin hankalin da wutarsa ke ruruwa a jirgin.

Da dama daga cikin bakin – hauren, wadanda akasari ‘yan Afirka ne suna fama da matsalar rikicewa da fargaba, sakamakon halin da suka shiga kafin ceto su, ga kuma halin rashin tabbas game da makomarsu, gashi kuma duk cikar su, suna amfani da ban – daki biyu ne kawai da ke cikin jirgi, wadda fadinsa bai wuce murabba’in mita 180 ba, kamar yadda Mr. Camps yayi bayani.

Wasu bakin – hauren sun fara yajin cin abinci, lamarin da ya sa kungiyar agaji ta Proactiva Open Arms din ta aike da tawagar masana halayyan dan adam da masu shiga tsakani don kwantar da hankula tsakanin fasinjojin jirgin da suka fito daga kasashe dabam – dabam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.