Liverpool ta lashe kofin Super League

Wasu 'yan wasa Liverpool da suka hada Sadio Mané a bangaren hagu da Mohamed Salah a tsakiya suna murnar lashe kofin zakarun Turai tare da mai horas da su Jürgen Klopet Andrew Robertson.
Wasu 'yan wasa Liverpool da suka hada Sadio Mané a bangaren hagu da Mohamed Salah a tsakiya suna murnar lashe kofin zakarun Turai tare da mai horas da su Jürgen Klopet Andrew Robertson. REUTERS/Carl Recine

Kungiyar Liverpool taci kofin ta na farko na wannan sabuwar kaka a daren Laraba, bayan da ta doke Chelsea a wasa daya tilo na neman cin kofin zakaran zakarun Turai wato super league.

Talla

Bisa al'adar wasan neman cin kofin zakaran zakarun Turai, akan zakulu kungiyoyin kwallan kafa biyu ne, wato wadda ta ci kofin zakarun Turai Champions League da kuma zakarar da ta lashe Europa League.

Karo na hudu kenan a tarihi kungiyar Liverpool ta dauki wannan kofin bayan wannan nasara da ta samu kan Chelsea da ci 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaron raga a birnin Istanbul na kasar Turkiya, bayan da aka tashi wasa canjaras wato 2-2 a tsawon fafatawar wa'adin minti 90, da kuma Karin lokacin minti 30 na raba-gardama.

Chelsea ce ta fara jefa kwallo a raga tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, ta hannun dan wasanta Olivier Giroud, to amma Sadio Mané ya farke jin kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokacin.

Liverpool ta yi wannan nasara ce wata biyu bayan Jurgen Klopp ya jagorance ta ta dauki kofin Zakarun Turai, a lokacin da ta doke Tottenham 2-0 a wasan karshe.

Mai tsaron ragar Liverpool Adrian ne ya haramta wa Tammy Abraham na Chealsea zura kwallo a bugun finaretin karshen wasa, abin da ya baiwa tawagar Jurgen Klopp dake rike da kambin zakarun Turai nasarar shiga kakar bana da kafar dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.