Italiya

Italiya ta kwashe marasa lafiya daga jirgin ceto bakin - haure

Jirgin Kungiyar agajin Spaniya daya isa gabar ruwan tsibirin Lampedusa
Jirgin Kungiyar agajin Spaniya daya isa gabar ruwan tsibirin Lampedusa AFP

Italiya ta kwashe wadanda ke fama da rashin lafiya daga jirgin agajin Spaniya mai dauke da bakin – haure zuwa gabar ruwan Lampedusa, yayin da jirgin ke jiran tsammani a tekun a yau Juma’a, duk da amincewar wasu kasashen Turai na karbar mutane 134 da ke cikin jirgin.

Talla

An yi ta gutsiri – tsoma tsakanin kungiyar agaji da jirgin ruwan ta da ke ceto bakin – hauren da ke tafiya mai hatsari a yankin tekun Mediterranean, da ministan cikin gidan Italiya mai tsatsauran ra’ayi Matteo Salvini, amma a wanna karo, rikicin ya koma tsakanin abokan hamayyar siyasar kasa.

Ana ta kai ruwa rana tsakanin jam’iyyar nan mai kyamar bakin – haure ta Salvini, da jam’iyyar adawa ta M5S kan batutuwa da dama har da na bakin hauren da aka ceto, wadanda aka hana su kaiwa ga gabar ruwan Italiya.

Salvini ya dauki tsautsaurar matsaya game da jibge bakin – hauren da aka ceto a Italiya, inda ya ke cewa bai kamata a ce Italiya ce ke daukar wannan nauyi ba.

Sai dai ya zuwa Alhamis, wasu kasashen Turai sun amince su karbi wadannan bakin – hauren da suka zaku su ga kansu a gabar ruwar wata kasar Turai, har ma hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar Dinkin Duniya ta yi na’am da wanna shawara ta rarraba bakin – hauren tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.