Amurka-Isra'ila

'Yar majalisar Amurka tayi watsi da tayin Isra'ila

Rashida Tlaib,'yar majalisar Amurka daga yankin Falasdinu, da ta yi watsi da tayin Isra'ila na bata damar shiga kasar.
Rashida Tlaib,'yar majalisar Amurka daga yankin Falasdinu, da ta yi watsi da tayin Isra'ila na bata damar shiga kasar. REUTERS/Brittany Greeson/File Photo

‘Yar majalisar wakilan Amurka Rashida Tlaib, ta yi watsi da tayin gwamnatin Isra’ila na bata damar shiga kasar domin ziyartar mahaifiyarta dake yankin yamma da kogin Jordan.

Talla

Tlaib ta bayyana sharuddan da Isra’ila ta gindaya mata kafin shiga kasar, a matsayin tauye hakki, abin kunya da kuma takaici.

A ranar Alhamis Isra’ila ta hana Ilhan Oumar da Rashida Tlaib ‘yan majalisar wakilan Amurka na farko mata Musulmi, shiga cikinta, saboda ficen da suka yi wajen sukar matakan da take dauka kan Falasdinawa.

Sai dai ranar Juma’a Isra’ilar ta baiwa Tlaib damar, bayan gindaya sharuddan cewa ba za ta yi Magana kan hakkokin Falasdinawa da gwamnatin Isra’ila ba, kuma tilas ta kaucewa duk wani al’amari na siyasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.