Isa ga babban shafi
Italiya

Ana zargin ministan cikin gidan Italiya da tauye hakkin 'yan ci rani

Wasu masu yawon bude idanu, yayin daukar hoton jirgin ruwan agajin Spain na Open Arms da ya ceto 'yan ci rani daga teku, a kusa tsibirin Lampedusa, na Italy. 17/8/2019.
Wasu masu yawon bude idanu, yayin daukar hoton jirgin ruwan agajin Spain na Open Arms da ya ceto 'yan ci rani daga teku, a kusa tsibirin Lampedusa, na Italy. 17/8/2019. Reuters/Guglielmo Mangiapane
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Masu gabatar da kara a Italiya, sun soma gudanar da bincike, kan ministan cikin gidan kasar Matteo Salvini, bisa zarginsa da amfani da karfin ikonsa ta hanyar da bata dace ba, bayan haramtawa jirgin ruwan agajin da ya ceto ‘yan ci rani daga teku shiga cikin kasar.

Talla

Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun sama bincike kan muryoyin da aka nada ta wayar tarho, na musayar bayanai tsakanin ma’aikatar cikin gidan kasar ta Italiya, da kuma jami’an tsaron gabar teku.

A ranar asabar, ministan cikin gidan na Italiya ya baiwa kananan yaran da basa tare da iyayensu guda 27, daga cikin ‘yan ci rani sama da 100 da aka ceto daga tekun Mediterranean damar shiga cikin kasar, inda yacesaura 107 za su ci gaba da zama a gabar tekun.

Cikin wasikar da ya aikewa ofishin Fira Ministan kasar ta Italiya, Salvini ya ce ya bada umarnin ne ba a son ransa ba, sai dai ya sha alwashin ragowar ‘yan ci ranin manya 105 da kuma yara biyu, za su ci gaba da zama a gabar tekun kasar, cikin jirgin ruwan agajin da ya ceto su, matakin da ya gamu da sukar kungiyoyin agaji.

Tun a ranar Alhamis Ministan cikin gidan Italiya ya bada umarnin hana ‘yan ci ranin 134, shiga kasar bayan isa gaf da tsibirin Lampedusa dake kudancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.