Isa ga babban shafi
Turai-Birtaniya

EU ta yi watsi da bukatar Firaministan Birtaniya kan Brexit

Firaministan Birtaniya, Boris Johnson
Firaministan Birtaniya, Boris Johnson Lorne Campbell/Pool via REUTERS
Zubin rubutu: Michael Kuduson | Azima Bashir Aminu
1 Minti

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi watsi da bukatar Firaministan Birtaniya, Boris Johnson na soke batun shamaki a kan iyakar Ireland a kokarin cimma yarjejeniyar ficewa daga Tarayyar Turai, inda ta bayyana zabin da Firaministan ya bayar a matsayin wanda ba zai samu karbuwa ba.

Talla

Tun a jiya Litinin ne Firaministan na Birtaniya Boris Johnson ya aike wasika ga shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk inda ya nanata kudirinsa na cewa Birtaniya ba za ta amince da abin da ya kira shamakin da ba ya bisa turbar dimokaradiyya.

Tun bayan da ya karbi ragamar mulki a watan da ya gabata, Johnson ya kafe cewa dole ne Birtaniyar ta fice daga kungiyar Tarayyar Turan a ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa ko da kuwa ba tare da kulla yarjejeniya ba.

A bangare guda tuni Firaministan ya fara shirye-shiryen tunkarar rudanin tattalin arzikin da ficewa ba bu yarjejeniya za ta haddasawa kasar.

Sai dai hukumar Tarayyar Turai ta yi watsi da tayin da Boris Johnson ya yi a wasikar da ya aike mata, inda ta bakin kakakin ta, Natasha Bertaud ta ke cewa, bai yi bayani filla-filla game da shirinsa da bukatun sa ba.

Takaddamar dai na zuwa ne a daidai lokacin da Johnson ke shirin yin tattaki zuwa Berlin da Paris, in da ya ke fatan jan hankalin Jagorar Jamus, Angela Merkel da shugaban Faransa Emmanuel Macron don taimakawa wajen yarjejeniyar ficewa daga kungiyar kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.