Kasuwanci

EU: Za mu yiwa Amurka raddi idan ta laftawa barasar Faransa haraji

Shugaban majalisar kungiyar kasashen Turai EU, Donald Tusk, yayin jawabi a taron kasashen G7 da Faransa ke karbar bakunci a Biarritz. 24/8/2019.
Shugaban majalisar kungiyar kasashen Turai EU, Donald Tusk, yayin jawabi a taron kasashen G7 da Faransa ke karbar bakunci a Biarritz. 24/8/2019. REUTERS/Christian Hartmann

Shugaban majalisar kungiyar kasashen Turai EU, Donald Tusk, ya ce za su maida martani kan Amurka, muddin ta aiwatar da barazanar da ta yi, na kakaba haraji kan barasar da Faransa ke shigarwa kasuwannin Amurka.

Talla

Gabannin tashi zuwa Faransa don halartar taron kasashen G7 ne Shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar lafta haraji kan barasa dawasu ababen shan da Faransa ke kaiwa kasar, a matsayin martani kan sabon harajin da Faransar ta kakabawa manyan kamfanonin sadarwa dake hada hada a kasar, mafi akasarinsu na Amurka, ciki harda Google, Amazon da kuma Facebook.

A ranar 11 ga watan Yuli, Faransa da sanya hannu kan dokar cazar harajin kashi uku na jimillar ribar da manyan kamfanonin sadarwa ke samu a Faransa, wadanda mafi rinjaye na Amurka ne.

Wannan mataki ne yasa a halin yanzu shugaban Amurka Donald Trump soma nazarin maida martanin lafta haraji kan giya da sauran ababen sha da Faransa ke kaiwa kasuwannin Amurka.

Wannan dambarwa tsakanin Amurka da Faransa dai kari ce kan wadda ta riga ta kullu tsakanin Amurka da sauran kasashen Turai, bayan da shugaba Donald Trump ta kakaba harajin kashi 25 da kuma 10 kan karafa da aluminium, da kasashen Turan ke kaiwa kasuwannin Amurka, sai kuma karin haraji kan ababen hawa, da amfanin gona da Amurkan ta lafta kan kayayyakin kasashen Turan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI