G7- Brazil

Gobarar dajin Amazon ta dauki hankalin taron G7

Wani sashi na dajin Amazon da mahaukaciyar gobarar daji ke ci gaba da konewa.
Wani sashi na dajin Amazon da mahaukaciyar gobarar daji ke ci gaba da konewa. REUTERS/Ueslei Marcelino

Gobarar dake kone daji mafi girma a duniya na Amazon na ci gaba da daukar hankali a taron kasashen G7 da ke gudana a Faransa, bayan da rahotanni daga Brazil suka ce an samu tashin karin gobarar a sassan Amazon da a yanzu adadinsu ya haura dubu tara.

Talla

Dajin na Amazon dake bangaren arewacin Brazil, shi ne daji mafi girma a duniya, la’akari da cewa yana da fadin sama da murabba’in kilomita miliyan 5, da ya ratsa ta cikin kasashe 9, inda daga nan ne kuma masana kimiya suka ce duniya ke samun kashi 1 bisa 5 na iskar Oxygen da dan adam ke shaka.

Wannan al’amari na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashen duniya gami da kungiyoyi kare muhalli ke dada matsin lamba ga shugaban Brazil Jair Bolsonaro, ya gaggauta kawo karshen gobarar dajin, dake zama daya daga cikin mafi muni a tarihi, bayan da ta kone sama da kadada dubu 200 na fadin kasa.

A ranar Juma’a shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya aike da dakaru zuwa dajin na Amazon domin taimkawa wajen kashe gobarar, a daidai lokacin da yake fuskantar matsain lamba daga kasashen duniya kan gaggauta daukar mataki.

Sai dai Bolsonaro ya soki yanayin da kasashe ke daukar iftila’in da kuma matsayar gwamnatinsa, inda ya ce bai kamata ayi amfani da damar wajen, daukar matakan matsi kan kasar ta Brazil ba, bayan da manyan kasashen Turai suka dakatar da shirin kulla gagarumar yarjejeniyar kasuwanci da ita, har sai an kawo karshen gobarar dajin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI