Birtaniya

Birtaniya ta ba da Euro Miliyan 10 don kashe gobarar dajin Amazon

Firaministan Birtaniya Boris Johnson,  yayin taron G7 a birnin Biarritz na kudancin Faransa.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson, yayin taron G7 a birnin Biarritz na kudancin Faransa. Neil Hall/Pool via REUTERS

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya yi alkawarin bayar da yuro miliyan 10 don taimakawa wajen kashe gobarar dajin Amazon da ta tayar da hankalin duniya, baya ga tallafawa kasashen da gobarar ta shafa.

Talla

Cikin sanarwar da Birtaniya ta fitar a yau Litinin dai dai lokacin da ake kokarin karkare taron G7 na kasashe 7 mafiya karfin tattalin arziki a Faransa, ta bayyana cewa, za ta bayar da kudaden nan ta ke wadanda za a yi amfani da su farfado dasassan dajin da gobarar ta shafa.

Matakin na Birtaniya dai na zuwa ne bayan a jiya Lahadi shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa manyan shugabannin duniya sun amince da taimakawa kasashen da gobarar dajin Amazon ta shafa cikin gaggawa.

Sanarwar ta Birtaniya ta ruwaito Firaminista Boris Johnson na cewa, duniya na sane da halin da dajin Amazon ke ciki dangane da ibtila’in gobara wanda ya zama wajibi a tashi tsaye wajen tallafawa ko kuma dai matsalar da gobarar za ta haifar ta shafi kasashe dadama..

Duk da kasancewar kashi 60 cikin dari na dajin Amazon na cikin kasar Brazil, dajin wani sashe ne na kasashe 8 da suka kunshi Bolivia, Colombia, Ecuador, French Guiana, Guyana, Peru, Suriname da kuma Venezuela.

Tun gabanin fara taron shugaba Macron ya sha alwashin sanya batun na gobarar dajin Amazon cikin manyan batutuwa da taron na G7 zai tattauna akai duk kuwa da kakkausar sukar da ya fuskanta daga shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro wanda ya zargi Macron da katsalandan a harkokin cikin gidan Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI