Kamfanoni 100 sun yi kaura daga Birtaniya saboda Brexit
Wallafawa ranar:
Kimanin manyan kamfanonin kasa da kasa 100 ne suka koma Netherlands daga Birtaniya, yayinda 325 ke shirin ficewa nan kusa sakamakon fargabar makomar tattalin azikin kasar bayan kammala ficewarta daga Kungiyar Tarayyar Turai.
Hukumar Kula da Zuba Hannayen Jarin Kasashen Ketare ta Netherlnad, NFIA ta ce, kamfanoni da masana’antun Birtaniya na nuna sha’awarsu ta komawa kasar.
Shugaban Hukumar ta NFIA, Jeroen Nijland, ya ce, kamfanonin na yin kaura daga Biraniya sakamakon fargabar makomar tattalin arzikinta a daidai lokacin da alamu ke nuna cewa, akwai yiwuwar ta raba gari da Kungiyar Tarayyar Turai ba tare da cimma wata yarjejeniya ba.
Wannan ne babban dalilin da ya sa kamfanonin ke komawa Netherlands domin zama sabuwar cibiyar kasuwancinsu a Turai. In ji Nijland.
Tuni dai kamfanoni 62 suka samar da guraben ayyukan yi har guda 2,500 a Netherlands bayan sun yi kaura daga Birtaniyar, sannan kuma suka zuba jarin da ya kai Euro miliyan 310.
A yanzu haka, kasar ta Netherlands za ta ci gaba da gogayya da manyan kasashen Turai da suka hada da Faransa da Jamus da Belgium da Ireland wajen zawarcin kamfanonin Birtaniya da ke ficewar daga kasar saboda Brexit.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu