Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta fitar da sunan wakiliya a Tarayyar Turai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Yoan Valat/Pool via REUTERS
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
2 Minti

Shugaba Emmanuel Macron ya bayar da sunan Sylvie Goulard mataimakiyar shugabar babban bankin Faransa a matsayin ‘yar takarar neman kujerar wakiltar kasar a majalisar kungiyar Tarayyar Turai, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da Macron ke neman mafita ta fuskar manyan kudirorinsa da suka kunshi kasuwanci da sauyin yanayi.

Talla

Wata majiyar Diflomasiyyar kasar ta Faransa ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, tun farko Sylvie Goulard ita ce zabin Macron a matsayin minister tsaro bayan nasarar zabensa a shekarar 2017 amma kuma tuhume-tuhumen hayar mataimaki a majalisa da ake kan jam’iyyarta ya tilasta mata ajje aiki tun gabanin rantsar da gwamnatin.

Matakin aikewa da sunan Sylvie Goulard mai shekaru 54 a cewar majiyar na da nufin samun cikakkiyar dama ga Emmanuel Macron wajen cimma muradansa na samar da sauye-sauye ta fannin kasuwanci da dumamar yanayi a nahiyar ta Turai.

‘Yar takarar ta Faransa Goulard, wadda kwararriya ce a yarukan Turanci jamusanci da kuma italiyanci na da cikakkiyar kwarewa a al’amuran da suka shafi gudanarwar majalisar ta Turai kasancewarta tsohuwar ‘yar majlisa kuma wadda ta yi fadi-tashi wajen hadewar Jamus waje guda a shekarar 1989 baya ga kasancewa mashawarciya kan al’amuran siyasa ga tsohon shugaban Majalisar Tarayyar Turai Romano Prodi.

A ranar 1 ga watan Nuwamba mai zuwa ne shugabar Majalisar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen za ta kaddamar da majalisar wakilan Turai ta yadda kowacce kasar Turai za ta bukaci samun wadatattun ayyuka ta hannun wakilanta.

Tun a sanarwar ranar 17 ga watan Yulin da ya gabata ne, Faransa ta bayyana bukatar ganin ta amfana da sabuwar majalisar ta fuskar cimma manyan muradanta da suka kunshi kasuwanci sauyin yanayi da kuma makamashi a nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.