Isa ga babban shafi
Italiya

An kafa sabuwar gwamnatin hadaka a Italiya

Jagoran jam'iyyar Democratic Party Nicola Zingaretti, da Fira ministan Italiya Giuseppe Conte tare da mataimakinsa Luigi Di Maio.
Jagoran jam'iyyar Democratic Party Nicola Zingaretti, da Fira ministan Italiya Giuseppe Conte tare da mataimakinsa Luigi Di Maio. AFP/Vincenzo PINTO, Alberto PIZZOLI
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman | Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Jam’iyyun Five Star Movement da Democrat Party sun cimma matsayar kafa sabuwar gwmnatin hadaka a Italiya, lamarin da ya hana gudanar da zaben gaggawa a kasar.

Talla

Jam’ iyyar 5 Star mai adawa da tsohon yayi, ta ce, Fira ministan Italiya mai barin gado, Giuseppe Conte, shi ne zai jagoranci gwamnatin hadakar, bayan da ya yi murabus sakamakon rushewar gwamnatinsa mai fafutukar kare muradun talakawa a farkon wannan wata.

Jam’iyyun biyu sun shafe tsawon lokaci suna musayar yawu game da amincewa da Conte a matsayin wanda zai jagoranci sabuwar hadakar ko kuma dai a gabatar da wani mutum daban.

Yarjejeniyar da jam’iyyun biyu suka cimma, za ta kawo karshen rikicin siyasar da jaridun kasar suka bayyana a matsayin mafi tsanani a tarihin kasar.

Koda yake, shugaban Jam’iyyar 5 Star, Luigi Di Maio ya gargadi cewa, dole ne mambobinsu su kada kuri’a ta shafin yanar gizo domin amincewa da duk wata yarjejeniyar da suka kulla da jam’iyyar Democratic Party ta masu tsaka-tsakin ra’ayi.

Da dai, bangarorin biyu sun gaza cimma matsaya, da shugaban kasar ya ayyana gudanar da sabon zaben gaggawa a kasar cikin watan Nuwamba.

Wannan rikicin siyasar ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke cikin matsin lambar amincewa da kasafin kudi nan da wasu ‘yan watanni masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.