Isa ga babban shafi

Mutane dubu 90 sun sake kamuwa da cutar kyanda a Turai- MDD

Wani yaro da ke karbar rigakafin cutar kyanda
Wani yaro da ke karbar rigakafin cutar kyanda Reuters
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu | Nura Ado Suleiman
1 Minti

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana sake bullar cutar Kyanda a nahiyar Turai, inda alkalumman da ta fitar suka nuna cewa, kimanin mutane dubu 90 ne suka kamu da cutar, daga watan Janairu, zuwa Yuni na shekarar da mu ke ciki.

Talla

Rahoton da hukumar lafiyar ta majalisar dinkin duniya ta fitar a yau Alhamis ya danganta sake bullar wannan cuta a Turai da nokewar dubban jama’a wajen karbar maganin rigakafin cutar ta Kyanda, kuma daga farkon shekarar nan zuwa karshen watan Yuni, adadin wadanda suka kamu da cutar a duniya ya ninka sau biyu idan aka kwatanta da 2018.

Rahoton na WHO ya kara da cewa, adadi mafi yawa na masu fama da kyandar a Turai, na kasar Ukraine, inda mutane sama da dubu 84 suka harbu, sai kuma Kazakhstan da Georgia, yayinda a Jamus aka tabbatar da kamuwar akalla mutane 400 da cutar ta Kyanda mafi akasarinsu yara.

Shugaban kwamitin hukumar WHO mai yakar cutar kyanda a Turai, Dakta Guenter Pfaff, yace a halin yanzu, kasashen Albania, jamhuriyar Czech, Girka da kuma Birtaniya, sun rasa matsayin da suke da shi a a baya, na samun nasarar kakkabe cutar kyanda tsakanin al’ummominsu.

A shekarar 2017, sakamakon wata kididdiga ya nuna cewa kimanin mutane dubu 110 suka mutu a sanadin cutar Kyanda a duniya, mafi akasari yara ‘yan kasada shekaru 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.