Isa ga babban shafi
Turai-Birtaniya

Majalisar dokokin Birtaniya ta bijirewa Borris Johnson

Borris Johnson Firaministan Birtaniya
Borris Johnson Firaministan Birtaniya Tobias SCHWARZ / AFP
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 min

Makwanni 6 kacal da hawa karagar mulki, Majalisar dokokin Birtaniya ta bijirewa shirin shugaban Jam’iyyar Konzabatib Borris Johnson ,wajen yi masa bore tare da wasu Yan Majalisun da suka fito daga Jam’iyyar sa, matakin da ya kauda jagorancin yawan yan majalisun da yake da shi.

Talla

Yan Majalisun Konzabatib 21 suka hada kai da yan adawa wajen kada Firaminista a Majalisardokokin Birtaniya da kuma shirin rubuta wata doka wadda zata hana kasar ficewa daga kungiyar Turai ba tare da kulla yarjejeniya ba da kuma jinkirta ficewar na Karin watanni 3.

Firaminista boris Johnson yayi barazanar cewar yan Majalisun Jam’iyyar sa da suka bijirewa shirin nasa zasu fuskanci kora daga Jam’iyyar, yayin da wani daga cikin su Philip Lee ya sauya sheka zuwa bangaren masu goyan bayan kungiyar Turai.

Bayan shan kaye a zaben wanda ya nuna cewar masu adawa da manufofin sa sun samu kuri’u 328, sabanin 301 da ya samu, Johnson yace bashi da abinda ya rage sai kiran sabon zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.