Isa ga babban shafi
Turai-Birtaniya

Kotu ta yi watsi da bukatar hana Johnson rufe majalisar dokokin Birtaniya

Firaministan Birtaniya Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris Johnson Peter Summers/Pool via REUTERS
Zubin rubutu: Michael Kuduson
1 min

Babban kotu a birnin Landan ta yi watsi da karar da aka shigar na kalubalantar Firaminista Boris Johnson kan kudirinsa na dakatar da zaman majalisar dokokin kasar daga mako mai zuwa.

Talla

Babban alkalin Ingila da Wales, Ian Burnett ya ce an kori wannan kara, bayan kalubalen da ya samu goyon tsohon Firaminista John Major.

Amma kotu ta ba da damar a garzaya da batun kotun koli, don daukaka kara, wadda za a saurara a ranara 17 ga watan Satumba.

Wata ‘yar gwagwarmaya, Gina Miller ce ta shigar da karar.

Ita ta taba samun nasara a kotun koli, lokacin da ta bukaci kotu ta tursasa wa gwamnati neman amincewar majalisar dokoki, kafin ta shiga tattaunawa da Tarayyar Turai.

Bayan wannan hukunci na kotu, ana fita waje Miller ta shaida wa manema labarai cewa da ita da tawagar lauyoyinta ba za su karaya ba, tana mai cewa don kowa da kowa suke wannan gwagwarmayar, har ma da al’umma ta gaba, don haka yin kasa a gwiwa zai kasance tamkar watsi da aikata abin da ya dace.

Hukuncin na Juma’ar nan ya baiwa Firaminista Johnson kwarin gwiwa, bayan kayen da ya sha a majalisar game da manufofinsa na barin Tarayyar Turai ko da yarjejeniya ko akasinta a 31 ga watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.