Isa ga babban shafi
Faransa

Zakara ya yi nasara a kotu

Corinne Fesseau da zakaranta Maurice
Corinne Fesseau da zakaranta Maurice Fuente: AFP.
Zubin rubutu: Michael Kuduson
2 Minti

Zakaran nan mai suna Maurice ya yi nasara bayan an gwabza a kotu kan karar da aka shigar na uwar dakinsa sakamakon yadda ya ke damun makwafta da cara, inda kotu ta ce ai shi ma zakaran na da damar yin cara  ko dada tsakar da tsakar rana ce.

Talla

Zakaran nan mai suna Maurice ya yi nasarar a Kotu bayan an gwabza a kotu kan karar da aka shigar na uwar dakinsa sakamakon yadda ya ke damun makwafta da cara, indakotu ta ce ai shi ma zakaran na da damar yin cara da tsakar rana.

Wannan kara da makwafatar uwar dakin Maurice, mai suna Corinne Fesseau suka shigar ta shahara a kafafafen yada labarai a sassan duniya, inda ake ganin cewa alamu ne na irin zaman tankiya da ke tsakanin mai zakara da makwaftan ta.

Lauyan Fesseau, uwar dakin zakara Maurice, Julien Papineau ta ce zakara ya yi nasara a kotu, kuma za a biya shi diyyar kudi har Yuro dubu 1.

Fesseau ta shaida wa kotu cewa babu wandaya taba yin korafi game da carar da zakaran ta Maurice ke yi, bayan da wasu ‘yan fansho suka suka sayi wani gida kusa da ita.

Jean – Louis wanda tsohon manomi ne damatars Joelle daga yankin Haute – Vienne a tsakiyar Faransa sun yi ikirarin cewa tun wajen karfe 4 na asuba Maurice ke damun su da cara.

Fesseau ta ce ta yi iya kokarin tadon gani zakaranta Maurice ya yi tsit amma abin ya ci tura.

Bayan hukuncin, a wajen kotun, Fesseau ta saka cara irin ta zakara don nuna farin cikin ta inda ta ke cewa ba ta san mai za ta ce ba, tana mai cewa ‘wannan nasara ce ga duk wanda ya ke cikin irin yanayin da na ke ciki’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.