Birtaniya

Firaministan Ingila na fuskantar koma-baya

Firaministan Birtaniya, Boris Johnson
Firaministan Birtaniya, Boris Johnson 路透社

Firaministan Birtaniya Borris Johnson na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga 'yan siyasar kasar dangane da batun ficewar kasar daga Kungiyar Tarrayar Turai, yayinda wasu daga cikin ministocin gwamnatinsa suka fara yin murabus.

Talla

Firaministan Johnson na ci gaba da fuskantar baraka a cikin gwamnatinsa, inda a  baya baya nan, Amber Rudd mai shekaru 56 mace da a shekara ta 2016 ta kada kuri’ar ci gaba da kasancewar Birtaniya cikin kungiyar Turai, ta ajiye mukaminta na minista daga wannan gwamnatin,inda ta bayyana gazawar gwamnatin da yanzu haka ke ci gaba da nisa da batun shiga tattaunawa da kungiyar Turai.

Wannan mata ta  yi Allah wadai ga shirin Firaministan na nuna karfin tuwo a duk lokacin da 'yan majalisar kasar suka nemi shiga tattaunawa ko muwahara da shi.

Nan take Firaministan kasar ta Birtaniya Borris Johnson ya nada 'yar majalisa Therese Coffrey a matsayin Ministan ayyuka da gajiyayyu na Birtaniya.

Ficewar Amber Rudd daga cikin gwamnatin kasar Birtaniya ,baraka da za ta yi wuya Borris Johnson ya dinke,yayinda wasu ke hasashen cewa Firamistan ya na sane da irin matsallolin dake jiran sa a wannan nauyin dake wuya sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.