Isa ga babban shafi
Rasha-Faransa

Faransa na fatan gyatta alakar da ke tsakaninta da Rasha

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da shugaba Vladimir Putin na Rasha
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da shugaba Vladimir Putin na Rasha REUTERS/Philippe Wojazer
Minti 2

Gwamnatin Faransa ta ce lokaci ya yi da za a samu sassaucin tsamin alakar da ke tsakaninta da Rasha bayan ganawar ministocinta da mahukuntan Kasar yau Litinin a Moscow, yayin ziyarar da ke matsayin karon farko da wani babban jami’i daga Faransar ya kai Rasha tun bayan kwace yankin Crimea a shekarar 2014.

Talla

Yayin ziyarar da Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian da na tsaro Florence Parly ke kaiwa yau a Moscow, Le Drian ya ce alamu sun nuna lokaci ya yi da za a samu sassaucin tsamin alaka tsakanin Faransar da Rasha, kasashe biyu da ke takun saka da juna.

A jawaban Le Drian gaban manema labarai yayin ziyarar wadda ke zuwa bayan Rashan ta amince da wani tsarin musayar fursunoni tsakaninta da Ukraine wanda ya farantawa Faransar, ya ce sun gamsu matuka da ganawarsu da ministocin kasar ta Rasha.

Itama ministar tsaron Faransar Florence Parly yayin jawabinta ta ce sun je Rashan ne a matsayin wakilai kuma bisa bukatar shugaba Emmanuel Macron da ke fatan sake kulla danganta mai cike mutuntawa da kuma fahimtar juna tsakaninsu da Rasha.

A cewar Parly, yana da matukar muhimmanci su kaucewa rashin fahimtar da ke tsakaninsu.

Tun bayan da Rasha ta kwace iko da yankin Crimea a shekarar 2014 ne, ta fara fuskantar tsamin alaka tsakaninta da kasashen Turai baya ga takunkuman da ta fuskanta daga Amurka da EU.

Shima ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce kulla alaka tsakanin Rasha da Faransa abu ne da ake bukata kuma ya zama wajibi.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ke kokarin ganin ya dawo da huldar Rasha cikin takwarorinta manyan kasashen duniya, bayan da yak arbi bakonci Vladimir Putin a Paris cikin watan Jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.