Birtaniya-Tarayyar Turai

Sarauniyar Ingila ta amince a jinkirta ficewar kasar daga EU

Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II
Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II . Eamonn M. McCormack/Pool via REUTERS

Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ta 2 ta amince da dokar da za ta tursasa wa gwamnati jinkirta ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai idan har ta kasa cimma yarjejeniya da Brussels, kamar yadda majalisar dattawar kasar ta bayyana.

Talla

Shugaban majalisar dattawar, Norman Fowler a sakon da ya wallafa a dandalin sadarwar Twitter, ya ce kudirin dokar ficewa daga Tarayyar Turai ya samu amincewar Saurauniya.

Ana ganin amincewar sarauniya a matsayin wani abu mai mahimmanci bayan gwamnati ta yi watsi da kudirin dokar.

An tsara kudirin dokar ne don taka wa Firaminista Boris Johnson birki kan alwashin da ya sha na fitar daBirtaniya daga kungiyar kasashen Turai ba tare da yarjejeniya da sauran kasashe 27 na yankin da za su saura a kungiyar ba.

A watan daya gabata Johnsonya bukaci Sauraniyar ta Ingila ta rufe majalisun dokokin kasar har sai ranar 14 ga watan Oktoba, inda yak e cewa hakan ya zama wajibi ne don ba shi damar gabatar da wasu manufofin cikin gida.

Amma hakan ya janyo tada jijiyoyin wuya daga ‘yan siyasa na kasar daga dukkan bangarori, inda suka bayyana matakin a matsayin kama karya da yi wa dimokaradiyya karan – tsaye.

Sai dai ana iya cewa Johnson ya zunguro sama da kara, saboda wanna mataki nasa ya janyo hadin gwiwar ‘yan adawa da ‘yan jam’iyyarsa majalisar dokoki amincewa da batun tilasta masa jinkirta ficewar kasar daga kungiyar Turai matukar ba cimma yarjejeniya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.