Turai

Ambaliya ta hana yara dubu 250 zuwa makaranta a Spain

Firaministan Spain, Pedro Sanchez
Firaministan Spain, Pedro Sanchez OSCAR DEL POZO / AFP

Ruwan sama mai karfin gaske ya sdauka a kudancin kasar Spain a daren jiya, inda ya haddasa gagarumar ambaliya a yanklin Valencia da yak ai ga rufe makarantu,lamarin da ya sa yanzu yara dubu dari 2 da 50 suka hakura da makarantar.

Talla

Ruwan saman da ambaliyar sun janyo rudani a hanyoyi, inda suka dakile harkar sufuri, saboda karfin ambaliyar ya fashe kogin Clariano, wanda ya zarta gabarsa har ya shiga gidaje, lamarin da ya sa yanzu jami’an agaji ke aikin kwashe mutane a yankunan da abin ya shafa.

Hotunan bidiyo sun nuna yadda ruwa ambaliyar ta yi awon gaba da motoci a garin Moixent, sannan ruwa mai karfi ya shiga tare da mamaye garin Ontinyent na kusa da shi, mai iyaka da Clariano, wadda hukumarv agajin gaggawan ta ce rabon da a ga ruwa mai karfi kamar haka tun shekarar 1917.

Ana shirin ko ta kwana a gaba daya yankin, kuma hukumomi sun ce sun sanya a rufe makarantu a kananan hukumomi 84, lamarin da ya shafi yara dubu 250.

Hukumar nazarin yanayi ta kasar Spain ta ce za a ci gaba da antaya ruwa kaman da bakin kwarya a kudanci Valencia da arewacin Alicante kuma mai yiwuwa ya ci gaba har ranar Juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.