Wasanni-Kwallon kafa

An yi mana rinto - Klopp

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp REUTERS/Charles Platiau

Mai horar da ‘yan wasan Liverpool Jurgen Klopp ya harzuka da yadda sakamakon wasa ya kasance a kashin da tawagarsa ta sha a daren Talata 2-0 a hannun Napoli, musammam  da bugun daga – kai – sai – mai tsaron raga da aka baiwa Napoli, wadda ya ce kuskure ne mai girma.

Talla

Sai dai bai musanta cewa ‘yan wasan sa ba su tabuka abin a zo a gani ba, inda ya ce ba su murza tamaula a matsayin da ya dace ba.

Liverpool ta yi rashin nasara 2-0, wadda hakan na nufin ta kasa daukan fansa kan Napoli, wacce ta doke ta a Italiya a kakar bara a hanyarta ta lashe gasar zakarun nahiyar Turai.

YADDA LIVERPOOL TA SHA KASHI

Bugun daga – kai – sai - mai tsaron raga da Dries Marten ya buga, da wata kwallo kusan karshen wasa daga Fernando Lllorente suka wargaza Liverpool a wasan rukuni na 5 na gasar zakarun nahiyar Turai da ta kara da Napoli a daren jiya Talata.

Dan wasan gaban na kasar Belgium din ya ci daga bugun daga – kai – sai – mai – tsaron – raga bayan dan wasan baya na Liverpool Andy Robertson ya rafke Jose Callejon, alkalin wasa ya hukunta Liverpool a kan haka.

Bayan nan ne kuma tsohon dan wasan Tottenham Llorente ya yi amfani da damar dakuskuren mai tsaron bayan Liverpool, Vergil Van Dijk ya samar ana daf da tashi ya makala wa mai tsaron raga na Liverpool din Adrian kwallo a zare, kuma aka tashi wasan a haka.

Da haka Liverpool ta kasaance kungiya ta farko mai rike da kambum gasar da ta sha kashi a wasan farko na gasar da ke biye, tun bayan AC Milan ta yi haka a shekarar 1994.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.