Jamus

Jamus za ta tallafa da Yuro biliyan 100 don yakar dumamar yanayi

Angela Merkel ta Jamus
Angela Merkel ta Jamus 路透社

Gwamnatin Jamus ta sha alwashin bada tallafin akalla Yuro biliyan 100 don yakar matsalar dumama ko sauyin yanayi, daga yanzu zuwa shekarar 2030.Matakin ya bayyana ne cikin wani daftarin kudurin da gwamnatin ta Jamus ke nazari akai.

Talla

Jam’iyyar Angela Merkel da ta ‘yan tsaka - tsaki masu sassaucin ra’ayi sun shafe daren jiya suna tattaunawar neman maslaha, gabanin sanar da manufar mai muhimmanci a ranar juma’a.

Kasar da ta fi kowanne karfin tattalin arziki a Tarayyar Turai, ta kasa kaiwa ga muradunta kan yanayi na shekara mai zuwa, amma ta dukufa haikan wajen cimma muradunta na 2030, wato rage kashi 55 na hayaki mai gurbata muhalli daga yadda yake a shekarar 1990.

Kere - keren kasar jamus kawai na samar da kashi 2 cikin dari na tururin da ke dimama yanayi a duniya tare da narka tsaunukar kankara da ke cikin tekuna, lamarin da ke haifar da tumbatsar tekuna a duniya.

Gwamnatin jamus na fatan kashe akalla euro biliyanb 100 daya karkashin wannan shiri na yaki da dumamar yanayi kafin shekarar 2030 kamar yadda kamfanin dillancin labaran faransa AFP ya ruwaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.