Iran-AMurka

Ko hoto ba zan dauka da Trump ba ballantana tattaunawa - Rouhani

Shugaban Iran,Hassan Rouhani
Shugaban Iran,Hassan Rouhani Reuters

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce kasar ba ta da shirin tattaunawa ko kulla wata yarjejeniya da Amurka, matukar ba ta janye takunkuman da ta kakaba mata ba, hasali ma baya ko bukatar daukar hoto tare da Donald Trump a taron Majalisar Dinkin Duniyar da ke ci gaba da gudana can a birnin New York.

Talla

A cewar Hassan Rouhani, duk da bukatar kasashen duniya na ganin an gana tsakanin Amurkan da Iran, jituwa ba za ta taba samuwa ba, matukar Tehran na ci gaba da fuskantar takunkumai ba gaira ba dalili daga Washington wadanda Donald Trump ya kakaba su don nuna kiyayya da kyashi.

Rouhani a jawabin da ya gabatar gaban zaman babban zauren Majalisar Dinkin Duniya wanda ke ci gaba da gudana a birnin Newyork na Amurka, ya ce ko hoto baya bukatar dauka da Trump domin a karshe tattaunawa da cimma matsaya ne ake bukatar hoton tarihi ba wai a farkon ganawa ba.

Rouhani wanda ya kira Trump da Mayunwacin hoto, ya ce ya na tantama game da bukatar Amurkan ta ganin ta gana da Iran yana mai cewa Amurka ba za ta taba samun karbuwa a wajensu ba, bayan ikirarinta na neman ganin bayansu, a don haka har kullum ta na matsayin makiyiya a garesu.

Cikin kalaman na sa, Rouhani ya kuma bukaci Saudiya ta kawo karshen yakin da ta ke yi a Yemen, yana mai cewa kisan da ta ke yiwa fararen hula bai isheta ba har sai da gayyato kasashe don luguden wuta kan mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Ka zalika Rouhani ya bayyana rundunar kawancen da Amurka ke shirin jagorantar kafawa a tekun fasha a matsayin wani yunkuri na sake ruruta rikicin yankin wanda ya zargi Saudiya da assasa batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.