Isa ga babban shafi
Faransa

Tsohon shugaban Faransa Jacques Chirac ya mutu

Tsohon shugaban Faransa, marigayi Jacques Chirac.
Tsohon shugaban Faransa, marigayi Jacques Chirac. AFP/Archives/PATRICK KOVARIK
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Tsohon shugaban Faransa, Jacques Chirac, wanda ya mulki kasar daga shekarar 1995 zuwa 2007 ya mutu yana da shekaru 86.

Talla

Tauraron Chirac ya soma haskawa a siyasar kasarsa da duniya, bayan zama magajin garin birnin Paris, daga shekarar 1977 zuwa 1995, daga bisani kuma ya zama Fira Ministan Faransa, inda daga nan aka zabe shi a matsayin shugaban kasar daga shekarun 1995 da 2002.

Tsawon lokacin da ya shafe yana shugabanci ya sa shi kafa tarihin zama shugaban Faransa mafi dadewa a karagar mulki, bayan tsohon shugaban kasar Francois Mitterrand.

A zamanin shugabancin Jacques Chirac, siyasa da manufofin kasashen ketaren Faransa, ya taimakawa kasar wajen samun kima a tsakanin kasashen Turai, da kuma kyautata alaka da Amurka.

Daga cikin abubuwan da ake tunawa da tsohon shugaban na Faransa akwai matsayar da ya dauka na fitowa fili wajen yin adawa da mamayar Amurka a kasar Iraqi cikin shekarar 2003.

A shekarar 2011 wata kotu a Faransa ta samu marigayi Jacques Chirac da laifin yin katsalandan cikin al’amuran gwamnati, cin amana, da kuma almubazzarancin kudaden gwamnati.

Duk da cewa ya musanta laifukan da aka zarge shi da aikatawa, tsohon shugaban bai daukaka kara don neman soke hukuncin ba, dan haka ne kotu ta yanke masa hukuncin dauri a gidan Yari da ba a zartas ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.