'Yan sandan Faransa sun tarwatsa zanga-zangar masu rigunan dorawa

Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Faransa
Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Faransa Zakaria ABDELKAFI / AFP

Jami’an tsaron Faransa sun sake arangama da masu zanga-zangar yaluwar riga da suka yi dafifi yau a wasu sassan kasar don kalubalantar salon kamun ludayin shugaba Emmanuel Macron.

Talla

A birnin Tolouse da ke kudancin Faransa, rahotanni sun bayyana cewa fiye da mutane dubu guda ne suka fita kan tituna, inda jami’an tsaro suka kame mutum guda bayan da ya yaga wata Fasta da gwamnati ta kafa don karfafa al’umma gwiwar taimako.

Masu zanga-zangar yaluwar rigar wadanda suka hade da masu zanga-zangar adawa da kin daukar mataki kan dumamar yanayi sun kuma rika kona tayoyi akan tituna.

Rahotanni sun bayyana cewa, sai baya da masu zanga-zangar suka fara kone-kone ne jami’an tsaron suka far musu ta hanyar harba musu hayaki mai sanya hawaye tare da ruwan zafi.

Zanga-zangar dai na zuwa ne kwanaki 2 bayan shugaba Emmanuel Macron ya gabatarwa Majalisa kunshin kasafin kudin shekarar 2020 wanda ya kunshe zaftare harajin gidaje biliyan 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.