Isa ga babban shafi

Faransa ta yi tir da matakin Iran kan kame Ruhollah Zam

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Iran Hassan Rohani
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Iran Hassan Rohani LUDOVIC MARIN / AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
2 min

Gwamnatin Faransa ta yi tir da matakin jami’an tsaron juyin juya halin Iran game da kame dan adawar Tehran Ruhollah Zam da ke samun mafaka a Paris jami’in da Iran ke zargi da shirya zanga-zangar bara baya ga kalubalantar tsare-tsaren gwamnatin kasar.

Talla

Cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar a Yau Laraba, ta ce abin takaici ne yadda jami’an tsaron juyin-juya halin na Iran suka kame Ruhollah Zam wanda ya bar Faransar kwanaki kalilan gabanin faruwar lamarin.

A cewar Faransar bata da masaniya game da yadda kamen ya gudana ko kuma inda Ruhollah Zam, yak e a halin yanzu, wanda tuni Iran ta bayyana shi a matsayin dan adawa bayan matakinsa na kalublantar tsare-tsarenta a shekarar 2018.

Ma’aikatar harkokin wajen ta Faransa, ta ce Zam na samun mafaka a kasar bayan gujewa mahukuntan Iran inda ya ke da cikakkiyar shaidar zama a Faransa, matakin da ke nuna cewa yana da cikakkiyar damar fita tare da shiga kasar a kowanne lokaci, kuma ya bar Paris a ranar 11 ga watan nan, amma kuma sanarwar jami’an ta biyo baya.

Ruhollah Zam ma’assasin tashar yanar gizo ta AmadNews jami’an tsaron juyin juya halin na Iran na kallonshi a matsayin dan adawa bayanda shafinsa yayi kaurin suna wajen caccakar aikinsu wanda suka ce ya na gudanar da aikinne bisa taimakon sashen fikira na Faransa.

Sanarwar Faransar ta nuna cewa babu shakka kasar za ta ci gaba da bibiyar halin da jami'in ke ciki don bayar da cikakkiyar kulawa da kuma kariya gare shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.