Isa ga babban shafi
Birtaniya

Majalisar Birtaniya ta tilasta Johnson neman karin wa'adin Brexit

Firayi ministan Birtniya Boris  Johnson, a Zaman Majalisar Birtaniya irinsa na farko mai matukar tarihi  tun bayan 1982
Firayi ministan Birtniya Boris Johnson, a Zaman Majalisar Birtaniya irinsa na farko mai matukar tarihi tun bayan 1982 PRU / AFP
Zubin rubutu: Salissou Hamissou | Azima Bashir Aminu
Minti 2

'Yan majaliasar dokokin Birtaniya a yau Asabar, sun kada kuri’ar amincewa da tilastawa Firaminista Boris Johnson, neman karin wa'adin ficewar kasar bayan da mambobin majalisar suka soki sabuwar yarjejeniyar da ya yi nasarar kullawa da kungiyar tarayyar turai a makon jiya.

Talla

Haka dai a zama wani, tarnaki ga Boris Johnson wajen yin gaban kansa na fitarda kasar ba tare da yarjejeniya ba, domin neman karin wa’adi lokacin raba garin.

Bukatar da dan majalisar Oliver Letwin ya gabatar, ta samu amincewar kuri’u 322 kan 306 da suka kada rashin amincewa da gyaran fuskar

Ga wadanda suka amince da gyaran fuskar zai baiwa yan majalisar damar samun lokaci mai tsawo da za su iya tattauna yarjejeniyar dake zama marar hadari koda ba a cimma yarjejeniya ba akanta a ranar 31 ga wannan wata na Octoba da muke ciki

Wannan ne dai karon farko tun bayan shekarar 1982 da Majalisar ta Birtaniya za ta gudanar da zama a ranar Asabar don tafka muhawara kan sabuwar yarjejeniyar ta Johnson wadda ya yi nasarar kullawa a ranar Alhamis.

Tun kafin zuwan yarjejeniyar gaban majalisa bangaren adawa suka fara kakkausar suka ko da dai Johnson ya bata tsawon sa’o’i 48 tun bayan kulla yarjejeniyar ya na shawo kan ‘yan majalisun jam’iyyarsa don ganin ba a samu matsala a zaman na yau ba.

Ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa ne dai wa’adin da Firaministan na Birtaniya Boris Johnson ya dibarwa kasar don karkare ficewa daga Turai a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.