Birtaniya

Gwamnatin Birtaniya za ta kira zaben gama-gari

Firaministan Birtaniya, Boris Johson a zauren majalisar dokokin kasar.
Firaministan Birtaniya, Boris Johson a zauren majalisar dokokin kasar. PRU / AFP

Fadar gwamnatin Birtaniya ta ce, Firaministan kasar, Boris Johnson zai gabatar da bukatar gudanar da zaben gama-gari muddin Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da tsawaita jinkirin ficewar kasar daga nahiyar har zuwa watan Janairu.

Talla

A ranar Talata ce, Johnson ya dakatar kudirinsa na Brexit bayan ‘yan majalisar kasar sun yi watsi da shirinsa na ganin an sanya hannu kan kudirin cikin kwanaki uku domin samun damar ficewa a ranar 31 ga wannan wata na Oktoba.

A halin yanzu, shugabannin  Kungiyar Kasashen Turai za su yi nazari game da yiwuwar kara wa Birtaniya wa’adin ficewa da kuma tsawon lokacin da hakan zai dauka.

Wasikar da doka ta tilasta wa Mr. Johnson aika wa Kungiyar EU bayan ya gaza samun goyon bayan da yake bukata, ta bukaci kara wa’adin ficewar kasar da watanni uku nan gaba.

A yanzu dai, fadar Dowing Street na duba yiwuwar kiran zaben gama-gari.

Kodayake dole ne majalisar dokokin kasar ta amince da matakin gudanar da zaben, amma a can baya, ‘yan adawa da ke majalisar sun bayyana aniyarsu ta kin amince wa da zaben har sai an yi watsi da batun ficewar Birtaniya ba tare da cimma yarjejeniya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.