Isa ga babban shafi
Faransa

Manoma sun yi zanga-zanga a Faransa

Manoman Faransa da ke zanga-zangar adawa da matakan gwamnati
Manoman Faransa da ke zanga-zangar adawa da matakan gwamnati AFP/Denis Charlet
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris
1 Minti

Daruruwan manoma a Faransa sun gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati saboda abin da suka kira matakan da take dauka da ke haifar musu da matsalar da ke sa wasu kashe kansu.

Talla

Daruruwan masu zanga-zangar dauke da rubuce-rubucen da ke bayyana cewar, ‘Macron, ka bamu amsa’ da ‘Anya Faransa na bukatar manoma kuwa?’ sun mamaye tituna domin bayyana irin halin kuncin da suka samu kansu a ciki.

Shugaban manoman Delphine Fernandez ya ce, suna bukatar ganin gwamnati ta kawo karshen irin matakan da take dauka da kuma yarjeniyoyin da take sanya hannu akai wadanda ke yi wa ayyukansu zagon kasa.

Fernandez ya ce, a kowacce rana, manomi guda na kashe kansa, kuma bisa dukkan alamu gwamnatin Emmanuel Macron ba ta san haka ba.

Ma’aikatar Lafiyar Kasar a watan Yulin da ya gabata ta ce, kisan kan da ake samu tsakanin manoma ya karu, inda a shekarar 2015 manoma 605 suka kashe kansu.

Ministan da ke kula da harkokin noma Didier Guillame ya ce, gwamnati na sauraron bukatun manoman, abin da ya sa ta amince da dokar da za ta ba su karfin fada aji wajen sanya farashin kayan da suke nomawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.