Birtaniya-Tarayyar Turai

Tarayyar Turai ta jinkirta ficewar Birtaniya da watanni 3

Michel Barnier, babban mai shiga tsakani na Tarayyar Turai kan ficewar Birtaniya daga Turai
Michel Barnier, babban mai shiga tsakani na Tarayyar Turai kan ficewar Birtaniya daga Turai REUTERS/Francois Lenoir

Tarayyar Turai ta amnice da jinkirta ficewar Birtaniya daga kungiyar da watanni 3, al’amarin da ya auku sa’o’i 90 gabanni ficewarta ba tare da yarjejeniya ba.

Talla

Yanzu dai wa’adin ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai ya koma 31 ga watan Janairun shekara mai kamawa, amma kasashe 27 na kungiyar na iya amincewa da ficewar ta kafin cikar wa’adin idan har ta cimma matsaya gabannin ranar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa yarjejeniyar ta yi bayanin cewa idan har Firaminista Boris Johnson ya samu hankalin majalisar dokokinsa don cimma matsaya kafin shekara mai zuwa, ficewa daga Turai ka iya kasancewa a ranar 30 ga Nuwamba ko 31 ga Disamba.

Sai dai wata sanarwa daga Tarayyar Turan na cewa, kafin nan, dole ne Birtaniya ta zabi wani babban jami’inta da zai yi aiki a hukumar Tarayyar Turai, kuma dole ya amince cewa ba za a sake tattauna yarjejeniyar ficewar da aka cimma ba.

Da yake barin wajen taron jakadun kasashen Turan, babban mai shiga tsakani na Tarayyar Turai, Michel Barnier ya ce ganawar ta yi matukar amfani, yana mai bayyana farin cikin cewa an cima matsaya.

Yau fiye da shekaru 3 kenan ‘yan Birtaniya suka bukaci ficewar kasar daga Tarayyar Turai a shekarar 2016 amma ana ta gutsiri tsoma tsakanin kasar da majalisar dokoki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.