Birtaniya

Birtaniya na kan gabar gudanar da zaben gaggawa

Firaministan Birtaniya Boris Johson
Firaministan Birtaniya Boris Johson PRU / AFP

Birtaniya na kan gabar gudanar da zaben gaggawa bayan babbar jam’iyyar adawa ta Labour ta ce, za ta goyi bayan shirin Firaministan kasar, Boris Johnson. Kodayake kawo yanzu ba a tsayar da ranar da za a gudanar da zaben ba.

Talla

Shugaban Jam’iyyar adawa ta Labour, Jeremy Corbyn ya ce, ya sha nanata cewa, a shirye suke su amince da shirin gudanar da zaben, kuma goyon bayansu ya ta’allaka ne kan janye butun ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai ba tare da cimma wata yarjejeniya ba.

Corbyrn ya ce, matakin da shugabannin kasashen Turai suka dauka na jinkirta ficewar Birtaniyar har zuwa ranar 31 ga watan Janairu, na nufin cewa, an cika sharadin da ‘yan adawar suka gindaya na jingine batun Brexit ba tare da yarjejeniyar ba.

A cikin sanarwar da ya fitar, jagoran ‘yan adawar ya ce, za su kaddamar da gagagrumin zazzafan yakin neman zabe don samar da ainihin sauyin da ba a taba gani a kasar ba.

Firaminista Johnson dai ya bukaci gudanar da zaben a ranar 12 ga watan Disamba mai zuwa, amma jam’iyyar Labour da sauran jam’iyyun adawa na matsin lambar ganin an gudanar da zaben a tsakankanin ranakun da ba su wuce 9 ga watan na Disamba ba.

Wani lokaci a yau ne Firaminista Johsnon zai gabatar da kudiri domin amincewa da zaben na gaggawa a kasar ta Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.