Isa ga babban shafi
Faransa

Wani dattijo ya kai hari kan Masallaci a Faransa

Jami'an tsaron Faransa sun killace harabar Masallacin da aka kai wa hari
Jami'an tsaron Faransa sun killace harabar Masallacin da aka kai wa hari GAIZKA IROZ / AFP
Minti 2

Jami’an ‘yan sandan Faransa sun cafke wani dattijo mai shekaru 84 da ake zargi da kai harin bindiga tare da jikkata mutane biyu da suka haura shekaru 70 bayan sun hange shi yana kokarin cinna wuta a kofar wani Masallaci.

Talla

Gwamnan Bayonne, ya ce, dan bindigan ya fara cinna wa wata mota wuta kafin daga bisani ya kama hanyar zuwa Masallacin da ke yankin kudu maso yammacin garin Bayonne .

Kawo yanzu babu cikakken bayani kan musabbabin kaddamar da wannan hari, yayin da aka bayyana mutumin a matsayin tsohon mamba a jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi da ke kyamar baki.

Jam’iyyar National Rally ta tabbatar cewa, maharin ya taba tsaya mata takara a shekarar 2015 a zaben yankuna kafin ta kore shi saboda wasu kalamai da ya furta da suka saba da manufofinta.

Tuni shugaban kasar, Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da harin, kuma ya lashi takobin daukar matakin hukunta masu kai farmaki, yana mai jaddada cewa, zai kare Musulmai a kasar.

“Faransa ba za ta amince da kiyayya ba “ in ji Macron.

Harin Masallacin na zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka zazzafar muhawara game da sanya kallabi tsakanin mata Musulmai a Faransa, dabi’ar da wasu ke adawa da ita a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.