Birtaniya

Za a sake sabon zaben 'yan majalisar Birtaniya a Disamba

Zauren Majalisar Dokokin kasar Birtaniya a birnin London. 12/3/2019.
Zauren Majalisar Dokokin kasar Birtaniya a birnin London. 12/3/2019. REUTERS

‘Yan majalisar dokokin Birtaniya sun amince da bukatar Fira minista Boris Jonson kan kudurin sake gudanar zaben zauren majalisar a ranar 12 ga watan Disambar dake tafe.

Talla

Matakin ‘yan majalisar dai goyon baya ne ga bukatar Fira Ministan kasar Boris Johnson na shirya zaben domin kawo karshen takaddamar siyasar kasar, da ta haddasa jinkirta ficewarta daga cikin kungiyar kasashen Turai har sau uku, sakamakon yin watsi da yarjejeniyar rabuwar ta Brexit da ‘yan majalisar suka yi a lokutan baya.

Matakin ‘yan majalisar na Birtaniya ya zo ne, sa’o’i kalilan, bayan da kungiyar kasashen Turai EU ta amince da matsar da lokacin cikar wa’adin ficewar Birtaniya daga cikinta daga 31 ga watan Oktoban da muke ciki, zuwa karshen watan Janairun shekarar 2020 dake tafe.

A farkon watan nan Fira Minista Boris Johnson yayi nasarar cimma sabuwar Yarjejeniyar Brexit da kungiyar EU, sai dai gaza amincewa da yarjejeniyar da ‘yan majalisarsa suka yi ya sa tilas ya nemi kara lokacin cikar wa’adin rabuwarsu da kungiyar kasashen Turan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.