Faransa

Guguwar Amelie ta yi wa mutane dubu 140 ta'adi a Faransa

Guguwar Amelie ta haddasa gagarumin igiyar ruwa mai karfin gaske a Kudu Maso Yammacin Faransa
Guguwar Amelie ta haddasa gagarumin igiyar ruwa mai karfin gaske a Kudu Maso Yammacin Faransa GAIZKA IROZ / AFP

Wata mahaukaciyar guguwa ta afkawa Kudu maso yammacin Faransa, inda ta haifar da gagarumar igiyar ruwa tare da tunbuke bishiyoy, lamarin da ya jefa mutane kimanin dubu 140 cikin rashin wutar lantarki.

Talla

Guguwar da aka yi wa lakabi da Amelie, wadda masana suka ce tana tafiyar kilomita 160 cikin sa’a daya, ta tumbuke tarin bishiyoyi da suka datse hanyoyin motoci da na jiragen kasa tare da tsinka wayoyin wutar lantarki.

Masu ayyukan agajin gaggawa da suka ce, sun kai dauki ga daruruwan mutane da suka bukaci agaji ta kiran waya, ba su tabbatar da rasa rai ba, sakamakon ifti’la’in, to sai dai rahotanni sun ce, wata tsohuwa mai kimanin shekaru 70, ta bace a Kudancin Nice, bayan da kasa ta zabtare a kusa da gidanta.

A kudu maso yammacin kasar, inda lamarin yafi kamari akalla mutane uku sun samu raunuka, galibi sakamakon rikitowar rassan itatuwa a kansu.

Jami’ai sun sanya kananan hukumomi akalla 14 na yankin cikin shirin ko takwana, yayin da guguwar ta Amelie ta zo ta ruwan sama mai karfin gaske.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI