Macron zai kulla yarjejeniyar Kasuwanci da China

Shugaban Faransa Emmaunel Macron da takwaran aikinsa Xi Jinping na China yayin taron kasashen G7 a Faransa
Shugaban Faransa Emmaunel Macron da takwaran aikinsa Xi Jinping na China yayin taron kasashen G7 a Faransa Ludovic MARIN / AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fara wata ziyarar aikin kwanaki 3 a kasar China, wace zata bashi damar kare kamfanoni da 'yan kasuwar Faransa da Turai domin samun damar Kara budin shiga kasuwanni kasar ta China, wanda haka ke zama babban makasudin ziyarar da Macron ya fara a Shanghai.

Talla

Ita dai wannan ziyara da ta fara da liyafar cin abincin dare, da kade kade da raye-raye a Shanghai, da shugaban kasar China Xi Jinping ya shiya wa shugabannin Turai da Latin Amurka a jajiberen taron bajon koli da kasar ke karban bakwanci duk shekara wanda shine karo na biyu.

Shugaba Macron ya ce, dan anjima kadan zasu kulla yarjejeniyar ta kasuwanci da China, wanda zai baiwa kasashen Turai fadada harkokin kasuwancin su da kasar, China, wanda zai saukaka shigar da wasu hajojin Nahiyar zuwa China, masamman manyan barasar kasar Faransa da Cukui.

Bayan bukin bajakolin na wannan Talata, ana kuma saran shugaba Macron ya sake ganawar keke-da-keke da Xi, a ranar Laraba a Beijin, inda zasu tattaunawa batutuwa da dama.

Duk da cewa masu masaukin baki, sun gargadi Macron da ya kaucewa batutuwan da suka shafi rikicin Hong Kong.

To sai dai mahukuntan Faransa sun ce, shugaban bazai yi kasa aguiwa ba, wajen jan hankalin mahukuntan Pekin kan tabbatar da dimokradiya a Hong-Kong da kuma batun daruruwan musulmai da aka tsare a arewa maso Yammacin China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI