Faransa

Faransa na zawarcin 'yan ci-rani domin ba su aiki

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron https://twitter.com/EmmanuelMacron

Gwamnatin Faransa ta bayyana wani shirin karbar ‘yan ci-rani da ke da kwarewa a fannoni daban-daban, tare da ba su damar samun ayyukan yi a cikin kasar, shirin da zai fara aiki a farkon shekara mai zuwa.

Talla

Ministar kwadago Muriel Pinacaud, wadda ke karin haske dangane da wannan shiri, ta ce siyasa ce da gwamnatin Faransa ke shirin aiwatarwa domin cike gibin kwararrun ma’aikata da kasar ke bukata kamar yadda ake yi a wasu kasashe da suka hada da Canada da kuma Australia.

Kafin nan, Firaminista Edouard Philippe ne, ya sanar da ministocinsa da kuma ‘yan majalisar dokokin kasar wani shirin gwamnatinsa kan yadda za a samar da tsari game da yadda ake karbar ‘yan ci-rani a kasar, bayan share kusan shekaru 8 ana kokorin fayyace irin mutanen da ya kamata a bai wa damar shiga Faransa don yin karatu da kuma samun ayyukan yi.

Shekaru 7 bayan kaddamar da shirin, Faransa za ta karbi dalibai dubu 500 daga kasashen waje don yin karatu tare da yiyuwar samun ayyukan yi a cikin kasar, wadda ita ce ta 5 a duniya da ta fi karbar daliban kasashen ketare.

To sai dai ga alama wannan shiri na iya haifar da rabuwar kawuna a cikin gwamnatin kasar ta Faransa, domin kuwa akwai wadanda ke adawa da yadda ake shirin aiwatar da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI