Rasha-Turai

Ana tsare da wani tsohon jami'in gidan yarin Rasha

Daya daga cikin gidajen yari a kasar ta Rasha
Daya daga cikin gidajen yari a kasar ta Rasha Getty Images

A Rasha ,masu bincike na tsare da wani tsohon jami’in dake aiki da wani gidan kurkuku, bayan samun sa da laifin karbar rashawa a lokacin gina daya daga cikin manyan gidajen yari mafi girma a Turai.

Talla

Masu bincike sun bankado ta yada tsohon jami’in da ya taba aiki a wani gidan yari a Rasha ya karbi akala milyan 10 na Euros a matsayin rashawa dangane da wani shirin na gina gidan yari na Turai mafi girma a yankin.

Jami’in mai suna Serguei Moiseenko da ya taba aiki a gidan yari na Saint Petersburg na tsare yanzu haka ,kasancewar bincike ya tabbatar da ya karbi makuden kudade daga wasu kamfanonin gine-gine dake da nauyin gina gidan yari mafi girma na Turai da aka yiwa sunan Kresty 2.

A shekara ta 2017 aka yi bikin kaddamar da wannan gida da aka kashe kudi akala milyan 170 na Euros da kuma aka share kusan shekara goma ana aikin ginin.

Tsohon jami’in zai iya fuskantar dauri na shekaru 8 zuwa 15 idan har aka tabbatar da cewa ya karbi rashawa wajen gina wannan gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI