Jamus

Jamus na bikin cika shekaru 30 rushe katangar Berlin

Al'ummar gabashin Jamus yayin tattakin hadewa da takwarorinsu na yammacin kasar, bayan faduwar katangar Berlin. 12/11/1989.
Al'ummar gabashin Jamus yayin tattakin hadewa da takwarorinsu na yammacin kasar, bayan faduwar katangar Berlin. 12/11/1989. REUTERS/Wolfgang Rattay/File Photo

Yau asabar Jamus ke bikin cika shekaru 30 da rushewa katangar Berlin da a baya ta raba kan bangaren yammacin kasar masu bin salon mulkin jari hujja, da kuma bangaren gabashin kasar masu ra’ayin gurguzu.

Talla

Ranar 9 ga watan Nuwamban shekarar 1989, aka shaidar rushe katangarta Berlin, daga lokacin ne kuma ake gudanar da bikin tunawa da ranar, wanda ake shafe mako guda ana yi.

Yayin gabatar da jawabi dangane da bikin, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta bukaci hadin kan kasashen Turai wajen tabbatar da karfin dimokaradiya, yanci da kuma kare hakkin dan adam.

A bangarensa, shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeire, yayin jawabi kan bikin tunawa da rusa katangar ta Berlin, ya bukaci Amurka ta rika mutunta kawancen da a baya ta kulla da kasashen duniya kan fannoni daban daban, ta kuma yi watsi da akidar fifita kai sama da komai, da shugaba Donald Trump ke aiwatarwa.

Daga birnin Washington, shugaban Amurka Donald Trump ya aike dasakon taya murna ga Jamus, gami da alkawarin ci gaba da aiki tare.

To sai bikin rushewar katangar ta Berlin ya zo ne a dai dai lokacin da alamun rarrabuwar kai tsakanin kasashen Turai ta bayyana kan kawancen kungiyar tsaro ta NATO.

A ranar Alhamis din nan, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, kungiyar tsaro ta NATO na shure-shuren mutuwa, lura da matsalar rashin fahimtar juna da ke tsakanin Amurka da sauran kasashen Turai, da kuma yadda Turkiya ta yi gaban kanta wajen kaddamar da farmaki a Syria.

Sai dai Shugabar Gwmantin Jamus, Angela Merkel ta yi watsi da kalaman na Macron, tana mai cewa, babu bukatar yanke wa kungiyar irin wannan hukunci na gaggawa ko da kuwa tana fama da matsaloli.

Shugaban kungiyar NATO, Jens Stoltenberg ya jaddaa cewa, har yanzu kungiyar na da karsashinta, sannan kuma Amurka da kasashen Turai na aiki tare fiye da yadda aka sani a can baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI