Spain-Catalonia

Al'umma na kada kuri'a a Spain

Firaministan Spain, Pedro Sanchez
Firaministan Spain, Pedro Sanchez REUTERS/Javier Barbancho

Al’uammar kasar Spain suna kada kuri’a a babban zabe na hudu cikin shekaru da dama, yayin da ake ci gaba da zaman dar – dar sakamakon gwagwarmayar ‘yan awaren Catalonia.

Talla

Sake gudanar da wannan zabe dai ya biyo bayan gaza samun goyon baya da Firaminista Pedro Sanchez ya yi ne daga sauran jam’iyyun siyasa, biyo bayan zaben watan Afrilu da bai kammalu ba, inda jam’iyyarsa ta Socialist party ta samu mafi rinjayen kuri’u, amma ta samu akasin haka a majalisar dokoki.

Sai dai bisa dukkan alamu dai kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba a zaben baya –bayan nan. Babu jami’iyyar da ake ganin za ta fi rinjaye a majalisar dokokin Spain mai kujeru 350 daga cikin jam’iyyun da ke takara a zaben.

Jam’iyyar masu ra’ayin gurguzu na iya samun galaba a zaben, amma za ta samu kasa da kujeru 123 da ta samu a zaben Afrilu. Jam’iyyar adawa ta masu ra’ayin mazan jiya kuwa na iya kara karfi a majalisar dokokin.

Da karfe 9 na safiyar Lahadi aka bude rumfunan zabe, kuma ana sa ran rufewa da karfe 8 na dare, inda ba za a dade ba sakamako zai fito.

Wannan zabe dai na zuwa ne a daidai lokacin da Spain ke kara samun rarrabuwar kawuna sakamakon rikicin ‘yan awaren Catalan da ya yi kamari a makonnin baya- bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.