Isra'ila-Falasdinawa

Gaza: za ku dandana kudar ku in kuka ci gaba da harba mana roka - Netanyahu

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu REUTERS/Ronen Zvulun

A yankin Zirin Gaza ana ci gaba da musayar wuta tsakanin dakarun Isra’ila da na mujahidai a Falasdinu, kwana na biyu a jere kenan, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 23, kuma babu alamun zai kawo karshe nan kusa – kusa.

Talla

An harba rokoki cikin Isra’ila, wadda hakan ya sa ta ta mayar da martani da hare – hare ta sama kan inda ta kira mabuyar mujahidai da dakaru masu harba rokoki a zirin Gaza.

An yi ta jin kugin jiragen yaki masu kai hare – hare, da karar fashe fashen wasu abubuwa, da 6arin wuta yayin da na’urorin kakkabo makamai ke baras da rokoki da makamai masu linzami.

A Zirin Gaza, mazauna yankin na auna irin barnar da aka haddasa musu tare da nuna alhinin wadanda suka rasu a wajen wani wurin adana gawarwaki da wani wurin jana’iza.

Majiyoyin diflomasiyya sun ce ana sa ran jakadar Majlisar Dinkin Duniya, Nickolay Mladenov ya sauka Masar don tattauna hanyoyin kawo karshen wannan gumurzu, sai dai wata majiya kusa da wannan tattaunawa ta yi kashedin cewa al’amura na iya dada rincabewa.

A jawabinsa na safiyar Laraba, Firaminista Benyamin Netanyahu ya ce dole ne dakarun kungiyar Islamic Jihad su daina kai harin roka yankinsa, ko su dandana kudar su, yayin da kakakin kungiyar, Musab al – Barayem ke cewa ba su da niyyar tattaunawa a yanzu ballantana sulhu, saboda martani suke mayarwa game da kisan babban kwamandan su Baha Abu al-Ata da mai dakinsa Asma da Isra’ila ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.