Ronaldo na daf da kafa wani sabon tarihi

Cristiano Ronalda sanye da jesin kasarsa Portugal
Cristiano Ronalda sanye da jesin kasarsa Portugal MIGUEL A. LOPES/LUSA

Cristiano Ronaldo na daf da kafa wani sabon tarihi, bayan nasar zura kwallaye uku rigis a wasar da kasarsa Portugal ta kara jiya da Lithuania, a wasannin neman gurbin shiga gasar kwallon kafar nahiyar turai a shekarar 2020.

Talla

A jumlarce ya ciwa kasarsa kwallaye 98 bayan kwallaye ukun da ya zuba a ragar Lithuania.

Ronaldo mai shekara 34 dake wasa kulob din Juventus ka iya zama dan wasa na biyu da zai kafa tarihin ci wa kasarsa kwallaye 100, idan har yayi nasar jefa kwallaye biyu a ragar Luxemberg a wasan da zasu yi ranar Lahadi mai zuwa.

Wannan ne dai shine karo na 9 da Ronaldo ke ci wa kasar sa kwallaye uku a jere, inda bakwai daga ciki ya yi su ne tun yana dan shekara 30.

kwallaye 11 kachal suka ragewa wa Ronaldo ya kamo dan wasan kasar Iran, Ali Daei, wanda ya kafa tarihin ciwa kasar sa kwallaye 109.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI