Faransa

Shugaba Macron dake tsakkiyar wa'adi bai da tabbacin lashe zaben 2022 mai zuwa

Shugaban Faransa  Emmanuel Macron ya cimma rabin wa'adin mulkinsa
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya cimma rabin wa'adin mulkinsa Reuteurs/Ludovic Marin via Pool

Macron da ya dare kan karagar shugabancin Faransa a ranar 14 ga watan mayun 2017 ya cimma rabin wa’adinsa tare da dan sakamakon da bai zaarta cikin cokali.Bayan wani lokaci na sauye sauyen tattalin arziki da basu haifar da wani canji ba da ya tunkari masu sanye da falmarori ruwan kwai da shi, ya kamata yanzu yak ara zage dantse wajen karawa kansa tagomashi da zai kara bashi damar tunkarar zaben 2022 a kasar har ma ya lashe shi .

Talla

A wannan lokaci na tsakkiyar wa’adinsa shugaba Emmanuel Macron na fuskantar kalubale mai girma wajen sake shawo kan Fransawa domin ganin ya sake maido da martabarsa da ta ragu a idon da dama daga cikinsu

Profesa Philippe Moreau Chevrolet, masani sadarwar da kuma kimiyar siyasa, shugaban cibiyar tuntuba da bada shawarwari ta MCBG , ya ce Emmanuel Macron ya fara rabin wa’adinsa na biyu ne, da burin ganin ya sake lashe zaben shugabancin kasar na 2022, ta hanyar ganin kamfato kashi 25% na faransawa masu zabe, kashi 1% cikin 3 na faransawan dake bangaren jam’iyun adawar kasar, Domin ganin ya yi nasarar lashe zaben na 2022 a gaban uwargida Marine Le Pen.

Emmanuel Macron na ganin ya zama wajibi ya yo kalar masu kada kuri’u, daga jam’iyu masu tsaurin ra’ayi a zagayen farko na zaben.

Wanda hakan ne ke sa shi yake maida hankali kan batutuwa masu tsauri musaman ma shi’anin da ya shafi baki 'yan ci rani.

Yanzu haka dai, shugaba Emmanuel Macron ya fara shirin tunkarar zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar da uwargida Marine Le Pen a 2022 bayan na farko da suka kara a 2017 a tsaaninsu, bisa tunanin samun kuri’un jam’iyun dake da ra’ayin tsakatsaki, saboda wata kila nakasun da yake kallon abukan hamayarsa da shi musaman Marin Le Pen ta jam’iyar masu tsatsaran ra’ayi ke da shi a idon Fransawa.

To sai dai lura da kwambalar 2017 da ya baiwa Le Pen Matsayi na biyu a fagen siyasar Fransa, da kuma kai ruwa ranar da gwamnatinsa ke ci gaba da yi da kungiyoyin kwadagon kasar dake nuna rashin amincewa da sauye sauyen da yake gabatarwa , za a iya cewa, sai ya kirshe wandonsa, domin kuma ya na da jan aiki a zaben na 2022.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI